Tawagar Majalisar Dinkin Duniya Zuwa Kasashen Yankin Sahel Ta Isa Kamar Mauritania
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i25079-tawagar_majalisar_dinkin_duniya_zuwa_kasashen_yankin_sahel_ta_isa_kamar_mauritania
Tawagar Majalisar dinkin duniya wacce ta kunshi mutane 15 ta isa kasar Maurintania a rangadin da suke yi zuwa kasashen Sahel guda 5.
(last modified 2018-08-22T07:00:52+00:00 )
Oct 21, 2017 08:25 UTC
  • Tawagar Majalisar Dinkin Duniya Zuwa Kasashen Yankin Sahel Ta Isa Kamar Mauritania

Tawagar Majalisar dinkin duniya wacce ta kunshi mutane 15 ta isa kasar Maurintania a rangadin da suke yi zuwa kasashen Sahel guda 5.

Tashar radio ta kasar France International ta bada labarin cewa tawagar ta isa birnin kasar Mauritani sannan ta bada labarin cewa shirin kafa rundunar yaki da ayyukan da ta'addanci a yankin yana tafiyar hawainiya a kasar ta Mauritani.

Florence Perlie, ministan tsaron kasar Faransa wanda yake ziyarar aiki a kasar Amurka tun jiya Jumma'a ya bayyana cewa dole ne gwamnatin kasar Amurka ta tallafawa rundunar G5 Sahel wacce ta hada dakaru 5000 daga kasashen Mali, Mauritania, Chadi, Niger da kuma Borkina Faso don yakar ta'addanci a yankin. 

Perlie ya kara da cewa idan Amurka taki yin haka sojojin faransa ne zasu wahala a yakin da suke da ayyukan ta'addancin a yankin na Sahel. Kasar Faransa ta jibge sojojinta masu yawa a arewacin kasar Mali tun shekara ta 2013 don hana ayyukan kungiyoyin ysn ta'adda a yankin.