DRC : MDD Ta Bukaci A Saki 'Yan Adawa A Lubumbashi
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i25133-drc_mdd_ta_bukaci_a_saki_'yan_adawa_a_lubumbashi
Majalisar Dikin Duniya, ta bukaci mahukunta a Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo dasu sallami 'yan adawa da ake tsare da a birnin Lubumbashi dake kudu maso gabashin kasar.
(last modified 2018-08-22T07:00:53+00:00 )
Oct 23, 2017 07:30 UTC
  • DRC : MDD Ta Bukaci A Saki 'Yan Adawa A Lubumbashi

Majalisar Dikin Duniya, ta bukaci mahukunta a Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo dasu sallami 'yan adawa da ake tsare da a birnin Lubumbashi dake kudu maso gabashin kasar.

Wata sanarwar da tawagar MDD a kasar cewa da (Monusco) ta fitar ta bukaci da a saki duk 'yan adawan da ake tsare da ba tare da wata wata ba, wanda a cewar sanarwar ya sabawa 'yancin walwala da na siyasa kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.

Babbar jam'iiyar adawa kasar ta (UDPS) ta ce mambobinta 48 ne aka cafke a lokacin da suke wani taro a birnin Lubumbashi.

'Yan sanda yankin dai sun zargi 'yan adawan da zagin shugaban kasar.