Sakatare Janar na MDD Na Ziyara A Afirka Ta Tsakiya
Oct 24, 2017 07:36 UTC
Yau Talata, babban sakatare MDD, Antonio Guterres ke fara wata ziyara ta kwanaki hudu a Afrika ta Tsakiya.
Wannan ziyara dai na zuwa ne a yayin da kasar ta Afrika ta tsakiya ke kara tsunduma a cikin rikicin kusan shekara guda da ya yi sanadin mutuwar daririwan mutane.
Mista Guteres zai fara ziyara ne daga yankin Bangansu inda rikici ya fi kamari a 'yan watannin baya bayan nan.
A watan Nowamba mai zuwa ne ake sa ran kwamitin tsaro na MDD zai sabunta aiki da yawan tawagarsa ta wanzar da zaman lafiya a wannan kasa ta jamhuriya Afrika ta tsakiya.
Tags