Jami'an Tsaron Aljeriya Sun Tarwatsa Wata Kungiyar Ta'addanci Mai Alaka Da Daesh
Jami'an tsaron kasar Aljeriya sun sanar da samun nasarar wata kungiyar ta'addanci da take da alaka da Da'esh da take aikinta a arewacin kasar.
Jaridar Al-Shuruq ta kasar Aljeriyan ta jiyo wata majiyar tsaron kasar tana fadin cewa jami'an tsaron sun sami nasarar kamawa da tarwatsa 'yan wata kungiyar ta'addanci da take da alaka da kungiyar Daesh a lardin Tizi Ouzou da ke arewacin kasar kafin su aiwatar da wani shiri na kai harin ta'addanci da suke da shi.
Majiyar ta kara da cewa 'yan wannan kungiyar suna da alaka da kungiyoyin ta'addanci da suke kasashen waje sannan kuma suna shirin kai hare-haren kunar bakin wake ne ga wasu cibiyoyi na tsaro na kasar kafin jami'an tsaron su sami nasarar cimma musu. Jami'an tsaron sun ci gaba da cewa suna neman shugaban kungiyar.
Ma'aikatar tsaron kasar Aljeriyan dai ta sanar da cewa tana ci gaba da daukan matakan tsaro hatta a garuruwa daban-daban na kasar a fadar da suke yi da ta'addanci.