Faransa : Dan Shugaban Equatorial Guinea Zai Sha Daurin Talala
Wata kotu a Faransa ta yanke wa babban dan shugaban kasar Equatorial Guinea, daurin talala na shekaru uku a gidan yari bayan da kotun ta same shi da laifin mallakar dukiya ta fitar hankali ba bisa ka'ida ba.
Kotun ta kuma bukaci tarar kudi ga Teodorin Obiang, ta Miliyan talatin na Yuro (Euro) bisa gina katsaitacen gida a Faransa, tare da bada umurnin a kwace duk kaddarorin da ya mallaka wanda ake rike da su ciki har da wani Otel na musammen a birnin Paris.
Laifukan da ake zargi Teodorin Obiang, wanda kuma shi ne mataimakin shugaban Equatorial Guinea, sun hada da hallata kansa da dukiyar al'umma, da karkata kudaden jama'a da cin amana da kuma cin hanci da rashawa.
Wannan dai ita ce shari'a irinta ta farko a faransa bisa harkar mallakar kaddarori ta hanyar da bata dace ba.