An Hallaka Mayakan Kungiyar Boko Haram A Arewa Maso Gabashin Najeriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i25203-an_hallaka_mayakan_kungiyar_boko_haram_a_arewa_maso_gabashin_najeriya
Kakakin dakarun tsaron Najeriya ya sanar da hallaka mayakan kungiyar boko haram cikin wani farmaki da sojojin kasar suka kai a arewa maso gabashin kasar
(last modified 2018-08-22T11:30:54+00:00 )
Oct 27, 2017 18:58 UTC
  • An Hallaka Mayakan Kungiyar Boko Haram A Arewa Maso Gabashin Najeriya

Kakakin dakarun tsaron Najeriya ya sanar da hallaka mayakan kungiyar boko haram cikin wani farmaki da sojojin kasar suka kai a arewa maso gabashin kasar

Kamfanin dillancin labaran Xin huwa na kasar China ya nakalto kakakin rundunar mayakan kasa na Najeriya Birgediya Janar Sani Usman Kuka-Sheka a wannan juma'a na cewa a jiya alkhamis sojoji sun kai wani sumame  dajin sambisa tare da samun nasarar hallaka mayakan kungiyar boko haram guda uku.

Birgediya Janar Sani Usman Kuka-Sheka ya kara da cewa a farkon wannan maku ma sojojin kasar sun hallaka mayakan boko haram 11 a arewa maso gabashin kasar.

Tun daga shekarar 2009 ne kungiyar boko haram ta fara kai hare-haren ta'addanci a Najeriya, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla dubu 20 tare da raba wasu sama da miliyan biyu da dubu 300 da mahalin su.