Wani Bom Ya Tarwatse A Yankin Mopti Da Ke Tsakiyar Kasar Mali
Nov 01, 2017 12:03 UTC
Majiyar sojin Mali ta sanar da cewa: Wani bom ya tarwatse a kan hanyar shigewar tawagar wakilin babban kotun kolin kasar a yankin Mopti da ke tsakiyar kasar ta Mali.
A bayanin da majiyar sojin Mali ta fitar a jiya Talata yana dauke da cewa: Wani bom ya tarwatse a kan hanyar shigewar tawagar wakilin babban kotun kolin kasar a yankin Mopti Abdurrahman Niang, inda tashin bom din ya yi sanadiyyar mutuwar sojojin Mali shida da wani farar hula guda.
Sai dai Abdurrahman Niang ya samu nasarar tsira da rayuwarsa, kuma babu wani rauni da ya samu, tuni dai jami'an tsaron kasar suka fara gudanar da bincike kan lamarin
Tags