Gwamnatin Tunusiya Ta Kirayi Jakadarta Da Ke Kasar Moroko
Gwamnatin Tunusiya ta bada sa'o'i 48 ga jakadarta da ke kasar Moroko kan ya dawo gida.
Gwamnatin Moroko ba ta bayyana dalilin kiran da ta yi wa jakadanta a kasar Moroko Muihammad Najim Al-Gharasali ba, amma akwai rade-radin cewa: Kotun sojin kasar tana zargin jakada Muhammad Najim Al-Gharasali da hannu a shirya makarkashiya kan tsaron kasa a lokacin da yake rike da ministan harkokin cikin gidan kasar ta Tunusiya musamman kan batun binciken da ya gudanar dangane da Shafiq Al-Jarayah wani shahararren dan kasuwa a kasar da kuma Sabir Al-Ajiliy tsohon shugaban hukumar yaki da ayyukan ta'addanci ta kasar.
Tun a ranar 17 ga watan Fabrairun shekara ta 2016 ne shugaban kasar Tunusiya Muhammad Beji Sebsi ya nada Muhammad Najim Al-Gharasali jakadar Tunusiya a kasar Moroko.