Harin Ta'addanci Ya Hallaka Dan Sandan Tunusiya.
Ma'aikatar cikin gidan tunusiya ta sanar da mutuwar daya daga cikin jami'an 'yan sandar biyu da 'yan ta'adda suka kaiwa hari a gaban majalisar dokokin kasar.
Kamfanin dillancin labaran kasar faransa ya nakalto ma'aikatar cikin gidan tunusiya a wannan alkhamis na cewa daya cikin jami'an 'yan sandar biyu da 'yan ta'adda suka kaiwa hari da karamin makami a gaban majalisar dokokin kasar ya rasa ransa sakamakon mumunan raunin da ya ji.
A ranar larabar da ta gabata ce, wani mutum ya kaiwa jami'an 'yan sandar dake tsaron majalisar dokokin kasar hari da karamin makami, cikin bayyanan da ma'aikatar cikin gidan tunusiyar ta fitar a yau, maharin na da tunani irin na 'yan ta'adda kuma ma yanada niyar hadewa da 'yan ta'adda a kasar Libiya domin haka jami'an tsaro suka kame shi.
Tunusiya dai da wasu kasashen arewacin afirka na fuskantar matsalar ta'addanci sakamakon guguwar siyasar 2011 da kuma shigar Amurka da kasashen yamma musaman ma jibke dakarun tsaron Nato da aka yi a kasashen.