Libya: An Yi Zanga-zangar Nuna Kin Amincewa Da Harin Garin Darnah
Nov 04, 2017 12:06 UTC
Mazauna garin Darnah a arewa maso gabacin kasar ta Libya sun yi Zanga-zangar ne ta yin Allah wadai da harin da aka kai wa garinsu tare da kashe fararen hula.
Bugu da kari masu Zanga-zangar sun yi tir da killace garin nasu da sojojin janar Halifa Haftar suka yi.
A daya gefen ma'aikatar harkokin wajen kasar Italiya ta bukaci da a gudanar da bincike akan laifukan yakin da aka tafka a cikin gari bayan gano gawawwakin mutane 36.
Tun bayan da kungiyar yarjejeniyar tsaro ta "Nato" ta kifar da gwamnatin Kaddafi a 2011, kasar Libya ta fada cikin rashin tsaro.
Kungiyoyin 'yan ta'adda da suka hada da Dae'sh sun kafa iko da wasu garuruwa na kasar ta Libya da suka hada da Darnah.
Tags