Tunisiya : Jam'iyyar Jamhuriya Ta Fice Daga Gwamnatin Hadin Kan Kasa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i25346-tunisiya_jam'iyyar_jamhuriya_ta_fice_daga_gwamnatin_hadin_kan_kasa
Jam'iyyar Jamhuriya ta kasar Tunisia wacce kuma ta dade tana cikin gwamnatin hadin kan kasa na kasar ta fice daga gwamnatin a yau Litinin .
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
Nov 06, 2017 18:55 UTC
  • Tunisiya : Jam'iyyar Jamhuriya Ta Fice Daga Gwamnatin Hadin Kan Kasa

Jam'iyyar Jamhuriya ta kasar Tunisia wacce kuma ta dade tana cikin gwamnatin hadin kan kasa na kasar ta fice daga gwamnatin a yau Litinin .

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ta nakalto Asim Asshabi babban sakataren jam'iyyar yana fadar haka a yau litinin . Asshabi ya kara da cewa sabani tsakaninta da jam'iyyar Annahda ta masu kishin addini wacce ita ma take cikin gwamnatin yana daga cikin dalilin da suka sa jam'iyyarsa ta yanke shawarar ficewa daga gwamnatin hadin kan kasa.

Jam'iyyar Jumhuriyya ta kasar Tunisia dai ita ce jam'iyyar siyasa mafi girma wacce jam'iyya mai mulki take hada kai da ita don gudanar da gwamnatin Yusuf Asshaheed. 

Jam'iyyar tana aiki tare da gwamnatin kasar Tunisa ne tun shekara ta 2012. kuma tana daga cikin jam'iyyun siyasan da suke goyon bayan gwamnatin Priminister Asshaheed.