Kungiyar Tarayyar Afrika Zata Rage Yawan Sojojinta Kimanin 1000 Daga Kasar Somaliya
(last modified Wed, 08 Nov 2017 06:56:30 GMT )
Nov 08, 2017 06:56 UTC
  • Kungiyar Tarayyar Afrika Zata Rage Yawan Sojojinta Kimanin 1000 Daga Kasar Somaliya

Kungiyar tarayyar Afrika ta sanar da shirinta na rage yawan sojojinta daga kasar Somaliya da yawansu zai kai kimanin dubu daya kafin karshen wannan shekara ta 2017.

Wani babban jami'in rundunar soji na kungiyar tarayyar Afrika da ya bukaci a sakaye sunansa ya bayyana cewa: Kungiyar tarayyar Afrika tana shirin fara janye sojojinta da suke aikin wanzar da zaman lafiya a kasar Somaliya kimanin dubu daya sakamakon ci gaba da tabarbarewan matakan tsaro a kasar. 

A karkashin shirin kungiyar tarayyar Afrika, kafin karshen shekara ta 2010, kungiyar tana da takaru dubu 22 amma kafin karshen wannan shekara ta ce zata rage sojoji 1000 dubu don rage asosrin da take yi a aikian .