Nijeriya Da E/Guinea Sun Cimma Yarjejeniyar Hadin Gwuiwa Ta Tsaro
Kasashen Nijeriya Da Equatorial Guinea sun sanya hannu kan wata yarjejeniyar tsaro kan kafa wani kwamitin hadin gwuiwa na tsaronteku da kan iyakoki da zai taimaka wajen fada da matsalolin tsaro da ake fuskanta da suka hada da fashi a kan teku, fasa kwabrin makamai, satar danyen man fetur da sauransu.
Rahotanni daga birnin Malabo, babban birnin kasar Equatorial Guinea sun bayyana cewar kasashen biyu sun cimma yarjejeniyar ce a karshen ziyarar da shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Buhari ya kai kasar Equatorial Guinea don ganawa da takwararsa na kasar Obiang Mbasogo inda bayan batun tsaro din shugabannin biyu suka tattauna kan yadda kasashen biyu za su fadada alakar da ke tsakaninsu a fagagen man fetur da iskar gas da kuma harkokin kasuwanci.
Fadojin shugabannin biyu sun bayyana cewar a yayin wannan ziyara ta kwanaki biyu, shugabannin biyu sun tattauna kan batutuwa na kasa da kasa da suka hada da batun fada da ta'addanci, tsaurin ra'ayi da kuma matsalar tattalin arziki da duniya take fuskanta wanda yake ci gaba da cutar da tattalin arzikin kasashen biyu.
A jiya Talata ce dai shugaba Buharin ya koma Abuja bayan wannan ziyara ta kwanaki biyu.