Senegal Ta Tabbatar Da Muhimmancin Tabbatar Da Tsaro A Nahiyar Afirka
(last modified Mon, 13 Nov 2017 18:55:41 GMT )
Nov 13, 2017 18:55 UTC
  • Senegal Ta Tabbatar Da Muhimmancin Tabbatar Da Tsaro A Nahiyar Afirka

Shugaban kasar ta Senegal Macky Sall ne ya jaddada wajabcin aiki domin tabbatar da tsaro a cikin kasashen Afirka.

Macky Sall ya bayyana haka ne a wurin taron kungiyar zaman lafiya da tsaro a birnin Dakar, karo na hudu.

Har ila yau, shugaban na kasar Senegal ya yi ishara da yadda aka murkushe kungiyar Da'esh a Iraki da Syria sannan ya kara da cewa; A halin da ake ciki a yanzu nahiyar Afirka tana fuskantar barazanar hare-haren daga kungiyar 'yan ta'addar da suka sha kashi.

Macky Sall ya kira yi kasashen Afirka da su nemo hanyoyin warware matsalolin da suke fuskanta.

Taron na Dakar yana samun halartar shugaban kasar Rwanda Paul Kagame, da na Mali Ibrahim Bubakar Keita.