MDD Ta Yi Gargadi Akan Take Hakkin Bil'adama A Kasar D-Congo:
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i25472-mdd_ta_yi_gargadi_akan_take_hakkin_bil'adama_a_kasar_d_congo
A jiya talata ne dai MDD ta yi gargadi akan yiyuwar amfani da karfi da akan 'yan adawa da za su yi Zanga-zanga a yau laraba.
(last modified 2018-08-22T07:00:59+00:00 )
Nov 15, 2017 03:13 UTC
  • MDD Ta Yi Gargadi Akan Take Hakkin Bil'adama A Kasar D-Congo:

A jiya talata ne dai MDD ta yi gargadi akan yiyuwar amfani da karfi da akan 'yan adawa da za su yi Zanga-zanga a yau laraba.

Kamfanin dillancin labarun Faransa da ya nakalto labarin ya ci gaba da cewa; Majalisar Dinkin Duniyar ta kira yi gwamnatin kasar ta D-Congo da ta kare hakkin 'yan kasa na yin taro kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.

Har ila yau, rundunar tabbatar da zaman lafiyar ta Majalisar Dinkin Duniya a kasar ta Demokradiyyar Congo,                ( Monosco) ya bukaci yan hamayyar da su kaucewa tayar da hankali a yayin Zanga-zangar tasu.

'Yan hamayyar siyasar sun shirya yin Zanga-zanga ne a yau laraba domin nuna kin yardarsu da jadawalin zabukan da aka shirya yi a kasar.

Jadawalin ya kunshi karawa shugaba Kabila wa'adin ci gaba da mulki har zuwa watan janairu na 2019.