An Zabi Sabon Shugaban Hukumar Zabe Na Kasar Tunisia
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i25476-an_zabi_sabon_shugaban_hukumar_zabe_na_kasar_tunisia
Majalisar dokokin kasar Tunisia ta zabi dan takatar neman shugabancin hukumar zaben mai zaman kanta na kasar, kuma dan jam'iyyar mai mulki ta Nida a matsayin sabon shugaban hukumar zaben.
(last modified 2018-08-22T11:30:59+00:00 )
Nov 15, 2017 12:19 UTC
  • An Zabi Sabon Shugaban Hukumar Zabe Na Kasar Tunisia

Majalisar dokokin kasar Tunisia ta zabi dan takatar neman shugabancin hukumar zaben mai zaman kanta na kasar, kuma dan jam'iyyar mai mulki ta Nida a matsayin sabon shugaban hukumar zaben.

Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya bayyana cewa majalisar ta zabi mohammad Altalili Al-munsuri dan jam'iyyar Nida mai mulki a matsayin sabon shugaban hukumar zaben kasar. A shekara mai zuwa ce ake saran za'a gudanar da zaben lardunan kasar. 

Kafin haka dai an shirya  gudanar da zaben ne a ranar 17 ga watan satumba shekara 2017 da muke ciki, amma jam'iyyun adawa kasar sun bukaci a dage zaben zuwa ranar 25 ga watan Maris na shekara ta 2018 mai kamawa..