An Yi Awan Gaba Da Wani Alkali A Kasar Mali
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i25514-an_yi_awan_gaba_da_wani_alkali_a_kasar_mali
Jami'an 'yan sandar kasar Mali sun sanar da sace wani alkali a tsakiyar kasar
(last modified 2018-08-22T11:31:00+00:00 )
Nov 18, 2017 05:51 UTC
  • An Yi Awan Gaba Da Wani Alkali A Kasar Mali

Jami'an 'yan sandar kasar Mali sun sanar da sace wani alkali a tsakiyar kasar

Cikin wata sanarwa da hukumar 'yan sandar Mali ta fitar a jiya juma'a, a daren Alhamis din da ta gabata wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun je gidan Soungalo Kone mai shar'a na yankin Segou dake tsakiyar kasar, suka kuma tafi da shi zuwa wani boyeyyen wuri.

Sanarwar ta ce mai yiyuwa wadanda suka sace alkalin kungiyoyin  ta'adda ne domin nuna rashin amincewarsu kan yadda ake gudanar da shara'a a cikin kasar.

Wannan lamari dai na zuwa ne bayan da Abdul Rahman Niang alkalin babbar kotun kasar ya tsallake rijiya da baya, bayan da 'yan bindiga suka bude masa wuta a garin Mopti dake tsakiyar kasar a ranar 31 ga watan oktoban da ya gabata.