Equatorial Guinea : Jam'iyya Mai Mulki Ta Lashe Lashe Zabe
(last modified Sat, 18 Nov 2017 11:19:59 GMT )
Nov 18, 2017 11:19 UTC
  • Equatorial Guinea : Jam'iyya Mai Mulki Ta Lashe Lashe Zabe

Jam'iyyar Demukuradiyya mai mulki ta (PDGE) a Equatorial Guinea, ta lashe mayan zabukan kasar da aka gudanar a ranar 12 ga watan nan na Nuwamba.

A sakamakon da hukmar zaben kasar ta fitar da yammacin jiya, Jam'iyyar ta (PDGE) ta lashe zaben da ya hada dana 'yan majalisar dokoki da sanatoci da kuma wakilan jihohi da kusan kashi 100% na yawan kuri'un da aka kada.

Jam'iyar ta lashe dukkan kujeru 75 na sanatoci.

Tun a shakara 1979 ne shugaban kasar, Teodoro Obiang Nguema, dan shekaru 74 ke shugabancin kasar.

wasu 'yan adawan kasar dai sun yi zargin cewa an tafka magudi da kuma kura-kurai a zaben.