AU Ta Yi Tir Da Cinikin Bakin Haure A Libiya
Nov 18, 2017 11:20 UTC
Shugaban kungiyar tarayya Afrika a wannan karo, kana kuma shugaban kasar Guinea, Alpha Conde, ya yi allawadai da cinikin bakin haure a kasar Libiya.
A cikin wata sanarwa da ofishin yada labarai na shugaban kasar Guinea ya fitar, Shugaba Conde ya yi tir da abunda ya danganta da tabi'ar dadadun shakaru da suka wuce.
Kungiyar ta AU ta kuma bukaci hukumomin kasar Libiya da su aiwatar da bincike don gurfanar da duk masu hannu a wannan mummunar harka gaban kotu.
Shugaba Conde ya ce wannan sabon salo na bauta dole ne a kawo karshensa, kuma kungiyar ta AU zatayi duk iya kokarinta na ganin hakan bata sake maimaituwa ba.
Tags