Mutane Shida Sun Rasa Rayukansu Sakamakon Harin Kunar Bakin Wake A Maiduguri
Rundunar 'yan sandan jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nijeriya ta bayyana cewa alal akalla mutane 6 sun rasa rayukansu ciki kuwa har da wasu 'yan kunar bakin wake su hudu, a wani harin kunar bakin wake na ta'addanci da aka kai yau din nan Asabar a kusa da birnin Maiduguri, babban birnin jihar ta Borno.
Rundunar 'yan sandan jihar ta Bornon ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar dauke da sanya hannun jami'in hulda da jama'a na rundunar Victor Isukwu, inda ta ce a safiyar yau Asabar ne wasu mata 'yan kunar bakin wake su biyu suka tayar da bama-baman da suka yi jigida da su a kusa da kauyen Alakaramtii da ke karamar hukumar Jere inda suka hallaka kansu.
Har ila yau sanarwar ta kara da cewa a wani harin na daban kuma da wasu mata 'yan kunar bakin waken guda biyu sukai kai kauyen da ke kusa da birnin na Maiduguri 'yan matan biyu sun hallaka kansu da kuma wani yaro karami baya ga wasu mutane hudu kuma da suka sami raunuka ciki kuwa har da mahaifiyar karamin yaron.
Wannan harin dai yana zuwa ne yayin da a shekaran jiya ma wasu 'yan ta'addan sun kai wani harin a jihar ta Borno lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar mutane 18 da raunata wasu guda 29.