Abinda aka sani Game Da Mummunan Harin Masar
(last modified Sat, 25 Nov 2017 06:02:21 GMT )
Nov 25, 2017 06:02 UTC
  • Abinda aka sani Game Da Mummunan Harin Masar

A halin da ake ciki an shiga zaman makoki na kwanaki uku a Masar bayan mummunan harin da ya yi ajalin mutum 235 da raunana wasu sama da 100 a masallacin Juma'a na al-Rawda dake lardin Bir al-Abedda a yankin arewacin Sinai.

Ganau sun ce an kai harin ne yayin da ake sallar Juma'a, inda da farko maharan suka yi wa masallacin kawanya da motoci, sannan suka dasa bam daga wajen masallacin, suka kuma datse duk wata hanyar fita daga cikin masallacin.

Bayan tayar da bam din da suka dana suka kuma soma bude wuta kan masu ibadar dake kokarin tserewa, suka kuma cinna wuta kan motoci jama'a don toshe hanyoyin kaiwa zuwa ga masallacin, da nufin kawo cikas wajen shigar motocin daukar marasa lafiya don kjai kai daukiwa wadanda harin ya rusa da su.

Wani da ya ji rauni a harin mai suna Magdy Rizk, ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP cewa, mahara 10 zuwa 20 ne sanye da kakin soji fuskokinsu a rufe suka kusa kai cikin wurin ibadar inda suka bude wuta kan masallatan.

Kuma a cewarsa dama iyalai da al'ummar yankin wadanda galibi ke bin akidar sufaye ne sun sha fuskantar barazana daga gungun mayakan masu tsatsaran ra'ayin addini.

Kawo yanzu dai babu wata kungiya data dau alhakin kai wannan harin, saidai tuni aka fara zargin reshen kungiyar 'yan ta'adda ta IS wacce ta yi kaurin suna wajen aikata ire-iren wadannan ayyukan ta'adi da kai wannan harin.

Kungiyar  IS dai na ganin Sufaye a matsayin wadanda akidarsu ta sha bamban da sauran Musulmi.

Reshen kungiyar IS a Masar ya jima yana kai hare-harensa kan jami'an tsaro a yankin Sinai, saidai kasancewar hare-harensa kan sojoji bai samun nasara sosai ya koma kan fararen hula musamen mabiya addinin Kiristoci da musulmi Sufaye.

Ko baya ga barazana 'yan ta'adda IS a yankin Sinai, Masar na fuskantar barazana da ga mayaka reshen Al'Qaida daga bangaren Libiya.

A halin da ake ciki dai shugaba Albdel fatah Al-Sisi na Masar ya sha alwashin maida martani mai karfi ga 'yan ta'addan.

Kawo yanzu dai duniya na ci gaba da nuna alhini da allawadai da harin na jiya Juma'a wanda shi ne irinsa mafi muni da aka taba gani a kasar ta Masar.

Shugaba Vladimir Putin na Rasha, ya danganta harin da abun takaici, a yayin da Shugaba Trump na Amurka Donald Trump ya yi tir da harin a yayin zantawa da takwaransa na Masar din.

Gwamnatin Jamhuriya musulinci ta Iran ita a ta yi allawadai da harin, tana mai cewa wannan harin ya kara tabbatar da cewa addinin muslunci daban akidar ta'addanci da sunan jihadi daban, domin kuwa hatta wuraren ibada na al'ummar musulmi da ake bauta ma Allah da ambatonsa, ba su tsira daga sharrin wadannan mutane masu dauke da wannan mummunar akida ba.

Suma gwamnatocib kasashen da suka hada Faransa, Biritaniya, Saudiyya, Isra'ila, Iraki da wasu kungoyoyi da cibiyoyin addinai irinsu Jami'ar Al-Azhar ta Masar da Paparomna Francis jagoran mabiya addinin Krista da kungiyar kasashen Larabawa duk sun yi tir da allawadai da harin.