Boko Haram ta kwace garin Magumeri na jihar Borno
Wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun karbe iko da garin Magumeri da ke arewa maso yammacin Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya nakalto mazauna garin na cewa wasu mahara da ake kyautata zaton 'yan boko haram ne sun kai hari cikin garin, lamarin da ya tilastawa mutane da dama yin hijra daga cikin garin.
Wannan shi ne hari na baya bayanan tun bayan harin kunar bakin wake da aka kai a wani masallaci na garin Mubi dake cikin jihar Adamawa, lamarin da yayi sanadiyar mutuwar mutane kimanin 60 tare da jikkata wasu da dama na daban.
Mayakan Boko Haram din sun kara zafafa hare haren da suke kai wa tun bayan daukewar ruwan sama a watan Satumba.
Wannan hari da aka kai garin na Mubi na daga cikin hare hare mafi muni da aka kai tun bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya hau kan mulki a shekarar 2015, inda ya yi alkawarin kawo karshen masu tada kayar baya.