Bakin Haure 33 sun nutse a tekun Libya
Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa a ranar assabar kimanin bakin haure 33 ne suka nutse bayan da jirgin ruwan da suke ciki, ya kife a gabar tekun Libya.
Cikin wani rahoton da ta fitar, majalisar dinkin duniya ta ce mutanen da abin ya rutsa da su suna kokarin ketarawa ne zuwa nahiyar Turai daga tekun baharum.daga cikin su akwai kananen yara da suka rasa rayukansu.
Rahoton ya ce an samu nasarar ceto mutane 60 daga hallaka cikin jirgin ruwan da ya nutse, sannan kuma an sake ceto mutane 140 a cikin wani jrgin ruwan na daban.
Idan ba a manta ba dai a ranar Alkhamis din da ta gabata, jami'an tsaron gabar tekun ruwan Libiya sun samu nasarar ceto bakin haure 250 daga hallaka, kamar yadda a ranar talatar da ta gabata jami'an tsaron ruwan Italiya suka ceto wasu 1100 daga 'yan ci rani dake son shiga cikin kasar ba kan ka'ida ba a tekun italiyan.