Kokarin Gwamnatin Sudan Na Karfafa Alakarta Da Kasar Rasha
A ziyarar aikin da shugaban Kasar Sudan ya kai zuwa kasar Rasha ya bukaci gwamnatin Rasha da ta dauki matakin kare kasarsa daga tsoma bakin kasar Amurka.
Sakamakon tarin matsaloli da kasashen nahiyar Afrika suke fuskanta a bangarori da dama gami da halin tsaka mai wuya da kasar Sudan ta shiga a fuskar tattalin arziki da na tsaro, a halin yanzu haka kuma kasar ta Sudan tana fuskantar wata babbar barazana daga kasar Amurka na kokarin ganin ta sake raba kasar ta Sudan zuwa kananan kasashe biyar, don haka shugaban kasar Sudan Umar Hasan Albashir ya bukaci kasar Rasha ta dauki matakin kare Sudan daga bakar siyasar Amurka.
Ziyarar aikin da shugaban kasar Sudan Umar Hasan Albashir ya kai zuwa kasar Rasha a makon da ya gabata shi ne irinsa farko a tsawon shekaru 60 da kasashen biyu suka kwashe suna gudanar da alaka a tsakaninsu, inda a yayin ganawarsa da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a ranar Alhamis da ta gabata a garin Sochi: Shugaba Umar Hasan Albashir ya tattauna batun kafa sansanin sojin Rasha a tekun Bahar Maliya tare da bayyana shirin gwamnatinsa na kulla yarjejeniyar hadin gwiwar soji da na fasaha da kasar ta Rasha.
Wannan bukata ta shugaban kasar Sudan Umar Hasan Albashir ga kasar Rasha ta zo ne bayan makonni kadan da gwamnatin Amurka ta dage takunkumin tattalin arzikin da ta kakaba wa kasar ta Sudan tsawon kimanin shekaru 20 da suka gabata, amma dai kasar ta Amurka bata cire sunan kasar Sudan daga cikin jerin kasashen da Amurka ta ce suna goyon bayan ayyukan ta'addanci a duniya ba.
Har ila yau daga cikin bukatun da shugaban kasar Sudan Umar Hasan Albashir ya gabatar ga mahukuntan Rasha akwai batun sayan makamai da kayayyakin noma daga kasar ta Rasha tare da yin kira ga gwamnatin Rasha kan ta dauki matakin sanya hannun jari a harkar makamashin Sudan da nufin ganin Rasha ta shigo an dama da ita a yankin domin zama garkuwa ga kasar Sudan musamman daga bakar siyasar Amurka.