Mali: An Dage Lokacin Gudanar Da Zabukan Kananan Hukumomi Zuwa 2018
Gwamnatin kasar ta Mali ta dage zabukan ne saboda sabanin da ya kunno kai a tskaninta da bangarorin da suka rattaba hannu akan yarjejeniyar sulhu ta 2015.
A wani bayani da majalisar ministocin kasar ta Mali ta fitar a jiya litinin, ta ce; Bayan ganawar da aka yi a tsakanin ministan safiyo na kasar ta Mali da bangarorin da za su shiga cikin zabuka, ya sanar da cewa an dage zabukan zuwa watan Aprilu na 2018.
Sanarwar ta ci gaba da cewa an dage lokacin gudanar da zaben ne domin a bada dama ga wadanda za su shiga a dama da su, su sami isasshen lokacin da za su shirya.
Mali tana cikin rikicin siyasa tun 2012 da aka yi juyin mulki wanda ya jawo bullar kungiyoyin 'yan ta'adda da kuma buzaye masu kokarin kafa kasar Azwad.