Kokarin Gwamnatin Kasar Sudan Na Karfafa Dangantaka Da Kasar Rasha.
Shugaban kasar Sudan ya bukaci gwamnatin kasar Rasha ta taimakawa kasar kan shishigin da gwamnatin Amurka take yi a cikin kasarsa.
Shugaba Umar Hassan albashir na kasar Sudan ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyarar aiki a birnin Moscow a makon da ya gabata, ya kuma bayyana cewa mafi yawan matsalolin da yankin gabas ta tsakiya da kuma kasarsa Sudan suke fama da su gwamnatin Amurka tana da hannu a cikin samar da su.
Wannan ziyarar ta shugaban Umar Hassan Al-bashir ta zo ne bayan kulla dangantakar jakadanci ta fiye da shekaru 60 tsakanin kasashen biyu.
Duk da cewa a cikin watannin baya kasar Sudan ta shiga tattaunawa da gwamnatin kasar Amurka kan takunkuman da Amurkan ta dora mata da kuma sanya ta cikin jerin kasashe masu goyon bayan ayyukan ta'addanci a duniya, Sudan ta sami sassauci inda Amurka ta janye wasu takunkuman da ta dora mata. amma duk da haka ta ci gaba da daukar gwamnatin kasar a matsayin mai tallafawa ayyukan ta'addanci a duniya.
Wani masanin harkokin tattalin arzikin a Jami'ar birnin Khartum na kasar Sudan, Mohammad Annayeer ya bayyana cewa dage wa kasar Sudan takunkumi wanda gwamnatin Amurka ta yi a baya bayan nan zai taimaka kwarai wajen tada komadar tattalin arzikin kasar.
Amma a ziyararsa zuwa kasar Rasha shugaba Al-bashir ya kulla wasu yerjiniyoyi da dama tare da gwamnatin kasar Rasha, wadanda suka hada da sayan kayakin yaki da kuma gyaran wasu da take su a gida wadanda suka dade ba'a yi masu gyara ba. Banda haka sudan tana bukatar ci gaba da sayan cimaka musamman alkama daga kasar Rasha,
Sai dai a bangaren gwamnatin kasar Rasha kuma, zata so karfafa dangantaka da kasar Sudan, don irin matsayin da kasar take da shi a nahiyar Afrika, har'ila yau akwai bukatar kamfanonin kasar Rasha su shiga kasar Sudan don amfana da dimbin arzikin karkashin kasa wadanda kasar take da su.
Wasu masana tattalin arziki suna ganin gwamnatin kasar Rasha zata fi amfanuwa da karfafa dangantaka da kasar Sudan don tana iya zama kofa ce ga kasar Rashar wajen shiga wasu kasashen Afrika wadanda suke bukatar kusanci da kasar musamman wajen zuba jari a fagagen tattalin arziki da ma'adinai.
Duk da cewa kasar Sudan tana fama da rikice-rikice na cikin gida amma wannan ba zai hana kasashen waje zuba jari a kasar ba, don ganin cewa ana samun zaman lafiya a mafi yawan yankunan arewacin kasar.