Afirka: "Yan Gudun Hijira 28 Sun Bace A Gabar Ruwan Moroko
Kungiyar 'yan gudun hijira ta duniya ce ta sanar da bacewar 'yan gudun hijirar ta bakin kakakinta Joel Millman.
Joel Millman ta kara da cewa; Wadanda suka bace din wani sashe ne na mutane 34 da kwale-kwalen da ke dauke da su ya tintsire. Tuni dai masu aikin ceto suka cetar da mutane 6 daga cikinsu.
Hukumar ta 'yan gudun hijira ta sanar da cewa a cikin shekarar bana kadai mutane 174 ne suka halaka a cikin ruwan da ke tsakanin kasashen arewacin Afirka da Spain.
An sami karuwar masu mutuwa akan ruwan idan aka kwatanta shi da shekarar da ta gabata da bai wuce 121 ba.
Bugu da kari, rahoton na hukumar da take kula da 'yan gudun hijirar ya ce; Zuwa 29 fa watan Nuwamba adadin 'yan gudun hijirar da suka shiga cikin kasar Spain sun kai 19,000 da 688.