Kamaru : A Shirye Mu Ke Mu Murkushe 'Yan A Ware_ Sojoji
Rundinar sojin Kamaru ta ce a shirye ta ke ta aiwatar da umurnin shugaban kasar Paul Biya na murkushe 'yan a ware a yankin masu amfani da turancin Ingilishi, a cewar ministan tsaro kasar, Joseph Beti Assomo.
Da yake bayyana hakan a gidan radiyon kasar, Mista Beti, ya ce a duk lokacin da shugaban kasa ya dauki wani matakin siyasa irin wannan, to babu wata makawa za mu aiwatar da shi.
A cikin wani jawabinsa na ranar Alhamis da ta gabata, shugaba Paul Biya, ya bayyana cewa kasarsa na fuskantar hare-hare daga wasu gungun 'yan ta'adda dake da'awar a ware, a matsayin maida martani kan kisan wasu sojojin kasar huhu da 'yan sanda biyu a yankin kudu maso yammacin kasar.
Gwamnatin kasar dai ta dora alhakin hare-haren ga 'yan fafatukar a ware a yankin masu amfani da turancin ingilishi, tana mai cewa ta dau duk matakan da suka dace na murkushe masu aikata wannan aika-aikar.