An Yi Suka Kan Dokar Hana Zanga-Zangar Lumana A Kasar Chadi
(last modified Thu, 07 Dec 2017 11:47:07 GMT )
Dec 07, 2017 11:47 UTC
  • An Yi Suka Kan Dokar Hana Zanga-Zangar Lumana A Kasar Chadi

Shugaban kungiyar kare hakkin bil'adama na kasar Chadi ya yi suka kan dokar hana zanga-zangar limani a kasar Chadi, wanda gwamnatin kasar ta kafa

Kamfanin dillancin Labaran kasar Faransa AFP ya nakalto Mohammad Nour Abdu shugaban wannan kungiyar yana fadar haka a jiya Laraba, ya kuma kara da cewa hakkin mutanen kasar Chadi ne su gudanar da zanga-zangar lumana. 

Nour ya kara da cewa idan gwamnatin kasar Chadi da kanta ba zata shirya zanga-zangar lumana na yin Allah wadai da matakin da Amurka ta dauka na sanya kasar cikin jerin kasashen da ta hana yayanta shiga Amurka ba, sauran mutanen kasar suna da damar shirya irin wannan zanga-zanag.

Daga karshe Mohammad Abdu ya kammala da cewa kungiyarsa zata shirya wata zanga zanga ta lumana nan ba da dadewaba don tabbatar da hakkin mutanen kasar na nuna ra'ayinsu kan wani abinda basaso.