Shugaban Kongo Na Kokarin Ta Zarce, 'Yan Adawa Na Zarginsa Da Magudi
(last modified Fri, 18 Mar 2016 16:43:46 GMT )
Mar 18, 2016 16:43 UTC
  • Shugaban Kongo Na Kokarin Ta Zarce, 'Yan Adawa Na Zarginsa Da Magudi

Shugaban kasar Kongo Sassou Nguesso na shirin sake ci gaba da shugabanci kasar a zaben jin ra'ayin al'ummar kasar da za ta gudanar a jibi Lahadi inda yake fatan al'ummar kasar za su ba shi da damar ci gaba da mulkinsa na shekaru 32 a kasar lamarin da 'yan adawa suka yi watsi da shi suna zarginsa da kokarin murguda sakamakon zaben.

Shugaba Sassou Nguesso, dan shekaru 72 a duniya, ya sanar da aniyarsa ta yin tazarcen ne bayan kwaskwarimar da aka yi wa kundin tsarin mulkin kasar a watan Oktoban da ya gabata inda aka cire bangaren da ya haramta wa duk wanda yake da sama da shekaru 70 a duniya shugabancin kasar da kuma rage tazarar da shugaban kasar zai yi kafin ya sake dawowa karagar mulki bayan yayi wa'adin mulkinsa sau biyu.

Magoya bayansa dai suna ci gaba da kiran da ya sake tsayawa takarar zaben suna masu bayyana shi a matsayin mutumin da ya kawo zaman lafiya a kasar.

A bangare guda kuma 'yan adawan kasar, a cikin wata sanarwa da suka fitar yau din nan Juma'a sun zargi shugaba Sassou Nguesso da kokarin murguda zaben don samun damar yin tazarcen kamar yadda suka ce yayi a zaben jin kuri'ar al'umma da aka gudanar a watan Oktoban bara don yin kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin kasar inda aka sanar da cewa kashi 94.3 na al'ummar kasar sun amince da yin kwaskwarimar.

Tun a shekarar 1979, shugaba Sassou Nguesso yake mulkin kasar Kongo duk da cewa a shekarar 1992 ya sha kaye a zabe amma dai ya sake dawowa ya dare karagar mulkin kasar har zuwa yau din nan.