An Kashe Wani Dan Jarida A Magadishu Babban Birnin Kasar Somalia
(last modified Tue, 12 Dec 2017 06:26:28 GMT )
Dec 12, 2017 06:26 UTC
  • An Kashe Wani Dan Jarida A Magadishu Babban Birnin Kasar Somalia

Wani dan jirada ya rasa ransa a lokacin da bom ya tashi a kusa da motarsa a birnin Magadishu babban birnin kasar Somalia a jiya Litinin.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ce Mohammad Ibrahim Gabu ya mutu ne a lokacin da wani bom wanda aka ajiye kusa da motarsa ya tashi da shi. Jami'an tsaro a birnin Magadishu sun tabbatar da wannan labarin amma ba su bayyana wanda ya kai hari kan wannan dan jaridar ba. 

Sai dai ana tuhumar mayakan kungiyar Al-shabab ne suka tada bom din don ganin cewa sun sha kai irin wadannan hare-hare kan kan mutane a cikin birnin. 

Kungiyar Al-shabab dai har yanzun tana iko da wasu kauyuka a kasar ta Somalia, sannan sukan kai hare-hare kan fararen hula a kasuwanni, ko kan jami'an tsaro na gwamnati da na tarayyar Afrika, ko kuma kan jami'an gwamnatin kasar.