Jami'an Tsaron Somaliya Sun Hallaka 'Yan Ta'addan Al-Shabab Guda 60
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i2629-jami'an_tsaron_somaliya_sun_hallaka_'yan_ta'addan_al_shabab_guda_60
Jami'an tsaro a yankin Puntland mai kwarya kwaryar cin gashin kai a kasar Somaliya sun sanar da samun nasarar hallaka wasu 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Al-Shabab su 60 a wani harin da suka kai musu da ya ba su damar kwace wasu yankuna da 'yan ta'addan suke rike da su.
(last modified 2018-08-22T06:58:00+00:00 )
Mar 18, 2016 14:19 UTC
  • Jami'an Tsaron Somaliya Sun Hallaka 'Yan Ta'addan Al-Shabab Guda 60

Jami'an tsaro a yankin Puntland mai kwarya kwaryar cin gashin kai a kasar Somaliya sun sanar da samun nasarar hallaka wasu 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Al-Shabab su 60 a wani harin da suka kai musu da ya ba su damar kwace wasu yankuna da 'yan ta'addan suke rike da su.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya jiyo gwamnan yankin Omar Abdullah da kuma wani jami'in 'yan sanda Manjo Mohamed Abdullah suna cewa jami'an tsaron sun sami nasarar hallaka wani adadi mai yawa na 'yan Al-Shabab din a gumurzun da ke ci gaba da gudana tsakanin bangarorin biyu a kusa da garin Baadqab, da ke kilomita 90 daga birnin Garowe babban birnin lardin na Puntland inda suke ci gaba da fatatttakan 'yan ta'addan daga yankin.

'Yan ta'addan dai sun kara kafuwa da ci gaba da ayyukansu ne a yankin na Puntland, wanda wani yanki ne mai girman gaske da ke arewacin kasar ta Somaliyan, tun bayan da aka fatattake su daga yankunan da ke kudancin kasar inda suka jima suna gudanar da ayyukansu daga can.

Gwamnatin kasar Somaliyan dai tana ci gaba da kiran gwamnatocin duniya da su taimaka mata a fadar da take yi da 'yan kungiyar Al-Shabab din wadanda suke ci gaba da gudanar da ayyukan ta'addanci a kasar da kuma kasashen makwabta irin su Kenya.