Ana Samun Tsanantar Tashe-tashen Hankula A Arewacin Kasar Mali
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i26411-ana_samun_tsanantar_tashe_tashen_hankula_a_arewacin_kasar_mali
Tashar telbijin din Faransa ta 5 ta bada labarin tsanantar fadace-fadace a cikin garin Kidal da ke arewacin Mali.
(last modified 2018-08-22T07:01:09+00:00 )
Dec 16, 2017 15:43 UTC
  • Ana Samun Tsanantar Tashe-tashen Hankula A Arewacin Kasar Mali

Tashar telbijin din Faransa ta 5 ta bada labarin tsanantar fadace-fadace a cikin garin Kidal da ke arewacin Mali.

rahoton ya ci gaba da cewa; Dakarun tabbatar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da ake kira da MINUSMA, sun  kutsa birnin domin gudanar da aikinsu na shimfida zaman lafiya.

Sai dai majiyar tsaro ta ce daya daga cikin dakarun na Majalisar Dinkin Duniya ya jikkata, ba tare da  bayyana wanda ya kai musu harin ba.

Arewacin kasar Mali dai yana fuskantar rikice-rikice ne duk da cewa an cimma yarjejeniyar tsagaita wutar yaki a tsakanin kungiyoyin da suke dauke da makamai a yankin.