Jam'iyyar ANC Za Ta Zabi Sabon Shugaba
A yau ne ake sa ran babbar jam'iyar ANC mai mulki a kasar Afirka ta kudu za ta fara zaben sabin shugabanin jam'iyar bayan da shugaba Jacob Zuma ya sauka daga kan kujerar shugabancin jam'iyyar.
A yayin da yake jawabi a gaban dubban magoya bayan jam'iyyar ta ANC , Shugaba Jacob Zuma ya tabbatar da komabayan da jam'iyyar ta fuskanta a shekaru 10 na jagorancinsa. ya ce al'ummar kasar ba ta gamsu da jam'iyyar da ke mulkin ba musamman kan batun cin hanci da rashin aikin yi da kuma miyagun ayyuka da suka karu a cikin shekaru 10 na mulkinsa.
Manyan ‘yan takarar shugabanci jam’iyyar sun hada da tsohuwar matar shugaba Zuma kuma tsohuwar shugabar kungiyar kasashen Afrika, AU, Dlamini-Zuma da mataimakin shugaban kasa Cyril Ramaphosa wanda babban dan kasuwa ne.
Taron mai tattare da kalubale duk wanda ya yi nasarar lashe kujerar shugabancin jami’iyyar shi zai kasance dan takarar shugaban kasar da za a gudanar a shekara ta 2019.
Wannan zabe dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake zargin shugabannin jam'iyyar ta ANC da laifin cin hanci.