WHO : Gabon Ta Murkushe Cutar Polio
Dec 17, 2017 11:11 UTC
Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta bayyana kawo karshen cutar shan-inna ko kuma Polio a kasar Gabon.
Wannan matakin dai ya biyo bayan shafe tsawon lokaci ba tare da samun wani sabon kamuwa ko kuma mai dauke da cutar ba a kasar.
Duk da hakan hukumar ta gargadi hukumomin kasar dasu kara zage dantse da kuma sanya ido akan hanyoyin yaki da bincike na cutar mai nakasa yara.
Hukumomin kiwon lafiya na kasar dai sun bukaci al'umma dasu ci gaba da kai ya 'yansu wajen karbar allurar riga kafin cutar da ba ta da magani sai dai hanyoyin riga kafi.
Tags