Jam'iyyar ANC Mai Mulki A Afirka Ta Kudu Ta Zabi Sabon Shugaba
Jam'iyyar African National Congress (ANC) mai mulki a kasar Afirka ta Kudu ta zabi mataimakin shugaban kasar Cyril Ramaphosa a matsayin sabon shugabanta wanda zai maye gurbin Shugaban kasar Jacob Zuma.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewa, sakamakon zaben da aka gudanar din dai wanda kakakin jam'iyyar ya fitar ya ce Mr Ramaphosa ya samu kuri'a 2,440 yayin da Ms Dlamini-Zuma, tsohuwar shugabar majalisar Tarayyar Afirka ta samu kuri'a 2,261, lamarin da ya ba wa Mr. Ramaphosa damar zama shugaban jam'iyyar wanda kuma ake ganin zai iya zama shugaban kasar a zaben da za a gudanar a shekara ta 2019.
Magoya bayan Mr. Ramaphosa dan shekaru 65 a duniya sun ta murna da nuna farin cikinsu dangane da sakamakon zaben wanda magoya bayan Dlamini-Zuma suka yi zargin an tafka magudi.
Sabon shugaban jam'iyyar ANC din dai ya yi alkawarin magance matsalar rashawa da cin hancin da ake zargin gwamnatin Zuma da shi lamarin da ya rage irin farin jinin da shugaban da kuma jam'iyyar ta ANC take da shi a idon al'ummar Afirka ta Kudun.