Shugaba Buhari Ya Tsawaita Wa'adin Shugabancin Manyan Hafsoshin Sojojin Nijeriya
Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya ya amincewa da tsawaita wa'adin shugabancin manyan hafsan hafsoshin sojin kasar saboda kokarin da suke yi wajen tabbatar da zaman lafiya da kuma kawo karshen ayyukan ta'addancin kungiyar Boko Haram.
Ministan tsaron Nijeriya Mansur Muhammad Dan-Ali ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da kakakinsa Kanar Tukur Gusau ya fitar , wanda ya ce an tsawaita wa'adin shugabancin manyan hafsoshin ne bisa la'akari da aiki tukuru da suke yi wajen kawar da Boko Haram da kawo zaman lafiya a yankin Naija Delta.
Manyan hafsan hafsoshin sojin da aka kara wa'adin shugabancin na su su ne: babban hafsan hafsoshin tsaro, Janar Abayomi Gabriel Olonishakin,babban hafsan hafsoshin sojin kasa Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai, babban hafsan sojojin ruwa Vice Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas da kuma babban hafsan sojin sama Air Marshal Baba Sadique Abubakar.
A watan Yulin shekara ta 2015 ne aka nada manyan hafsoshin sojin na Nijeriya a kokarin da sabuwar gwamnatin Muhammadu Buhari ta Nijeriya take yi na cika alkawarin da ta yi na kawo karshen kungiyar Boko Haram da kuma tabbatar da zaman lafiya musamman a yankin Arewa maso gabashin kasar wanda ya zuwa yanzu dai ana iya cewa an samu gagarumar nasara a wannan bangaren.