An Kama Tarin Makamai A Jami'ar Birnin Bamako
Jami'an yan sanda sun kama tarin makamai da suka hada da bindigogi a jami'ar Bamako babban birnin kasar Mali.
A wani samame da suka kai jami'ar birnin Bamako, biyo bayan wani fada a tsakanin daliban, jami'an 'yan sandar Mali sun kama wasu dalibai 16 tare da wasu tarin makamai da suka hada da kananan bindigogi masu sarrafa kansu kirar gargajiya guda 20 da harsashai 19 da adduna 63 da wukake 208 gami da sanduna guda shida.
Rikicin dai ya samo tushe ne daga zaben magatakardan kungiyar dalibai na sashen ilimin kimiya da fasaha na jami'ar.
A cikin wata sanarwa da ta fitar jiya Alhamis , ma'aikatar ministan tsaron kasar Mali ta ce fadan yayi sanadiyar mutuwar dalibi guda sakamakon harbinsa da aka yi da bindiga.