Jami'an Tsaron Tunusiya Sun Tarwatsa Wata Kungiyar 'Yan Ta'adda A Kasar
Ma'aikatar cikin gidan kasar Tunusiya ta sanar da cewa jami'an tsaron kasar sun sami nasarar tarwatsa wata kungiyar 'yan ta'adda ta mutane 9 larduna "Susa" da "Al-Qirawan" da kuma "Manuba" da ke kasar.
Kamfanin dillancin labaran Hukumar Gidan Radiyo da Talabijin na Iran ya bayyana cewar Ma'aikatar cikin gidan kasar Tunusiyan ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Juma'a inda ta ce binciken da aka gudanar na nuni da cewa 'yan wannan kungiyar suna da alaka da kungiyar ta'addancin nan ta Al-Qa'ida sannan kuma suna cikin shirya wani shiri ne na kai harin ta'addanci a kasar.
A shekara ta 2012 ne dai bangaren kungiyar al-Qa'ida na kasar Tunusiya ya fara ayyukansa na ta'addanci a yankin al-Sha'anabi da ke cike da duwatsu da ke kan iyakar kasar da kasar Aljeriya inda suka ci gaba da kai hare-haren ta'addanci musamman kan sojojin kasar.
Rahotanni sun bayyana cewar cikin watanni bakwai na wannan shekarar, jami'an tsaron kasar Tunusiyan sun sami nasarar kawo karshen wasu shirye-shiryen ta'addanci kimanin 828 kamar yadda kuma sun sami nasarar gurfanar da mutane 831 a gaban kotuna daban-daban bisa zargin da suka shafi ayyukan ta'addanci.