An Fara Zartar Da Yarjejjeniyar Tsagaita Wuta A Sudan Ta Kudu.
An fara zartar da yarjejjeniyar sulhun da aka cimma tsakanin gwamnatin sudan ta kudu da 'yan tawaye a safiyar yau Lahadi.
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya habarta cewa a safiyar yau Lahadi, an fara zartar da yarjejjeniyar sulhu tsakanin gwamnatin Salva Kiir da 'yan tawayen dake biyayya ga tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar da aka cimma a ranar Alhamis da ta gabata a hedkwatar kungiyar tarayyar Afirka dake birnin Addis Ababa na kasar Habasha.
Wanan yarjejjeniya na zuwa ne bayan kwashe da shekaru 4 na yakin basasa a kasar Sudan ta kudun.
Tun bayan da Riek Machar ya yi murabus daga kan mukaminsa na mataimakin shugaban kasa a shekarar 2013, kasar sudan ta kudu ta fada cikin yakin cikin gida, lamarin da yayi sanadiyar mutuwar dubban mutane tare kuma da raba wasu sama da miliyan biyu da mahalinsu.