Mali: Tsohon Shugaban Kasa Adamu Tomani Turi Ya Koma Gida
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i26673-mali_tsohon_shugaban_kasa_adamu_tomani_turi_ya_koma_gida
Kamfanin dillancin labarun Faransa ya ambato cewa; tsohon shugaban kasar ta Mali tare da iyalansa sun koma gida, kuma pira ministan kasar ne ya tarbe su a filin saukar jirgin sama na Bamako
(last modified 2018-08-22T07:01:11+00:00 )
Dec 24, 2017 15:26 UTC
  • Mali: Tsohon Shugaban Kasa Adamu Tomani Turi Ya Koma Gida

Kamfanin dillancin labarun Faransa ya ambato cewa; tsohon shugaban kasar ta Mali tare da iyalansa sun koma gida, kuma pira ministan kasar ne ya tarbe su a filin saukar jirgin sama na Bamako

A ranar juma'ar da ta gabata ne dai shugaban kasar ta Mali Ibrahim Bubakar Kaita, ya ce; Lokaci ya yi da zan fadawa dan'uwana Amadu Turi cewa ka dawo gida."

A na kuma sa ran cewa tsohon shugaban kasar zai gana da shugaba Bubakar Kaita a fadar gwamnati.

A shekarar 2002 ne dai aka kifar da gwamnatin Amadu Turi ta hanyar juyin mulki, ya kuma bar kasar ta Mali zuwa kasar Senegal inda ya yi zaman gudun hijira.