Ziyarar Shugaban Kasar Turkiya Zuwa Wasu Kasashen Afirka
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i26691-ziyarar_shugaban_kasar_turkiya_zuwa_wasu_kasashen_afirka
Shugaban Kasar Turkiya ya fara ziyara a wasu kasashen Afirka da nufin inganta alakar siyasa da tattalin arziki.
(last modified 2018-08-22T11:31:11+00:00 )
Dec 25, 2017 12:21 UTC
  • Ziyarar Shugaban Kasar Turkiya Zuwa Wasu Kasashen Afirka

Shugaban Kasar Turkiya ya fara ziyara a wasu kasashen Afirka da nufin inganta alakar siyasa da tattalin arziki.

A jiya Lahadi ne Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiya ya fara ziyarar aiki ta kwanaki biyu a wasu kasashen Afirka inda ya fara da kasar Sudan sannan kuma zai wuce zuwa kasashen Chadi da Tunusiya.

A yayin saukar sa a filin jirgi na birnin Khartoum, shugaban Erdogan ya samu kyakkyawan tarbe daga takwaransa  Al-Bashir na kasar Sudan, inda suka tabbatar da fadada alakar su a fanin tattalin arziki da siyasa.

 Shugabanin biyu sun sanya hannu a kan yarjejeniyar da ta shafi harkokin tsaro, ma'adinai, Noma, ilimi, yawan buda ido da sauransu.

har ila yau shugabanin biyu sun tattauna kan batun birnin Qudus, sannan a yau Litinin ake sa ran shugaba Erdogan zai wuce kasar Chadi daga can kuma zuwa kasar Tununsiya a gobe Talata.