Shugaba Deby Ya Yi Wa Gwamnatinsa Garambawul
(last modified Tue, 26 Dec 2017 11:04:17 GMT )
Dec 26, 2017 11:04 UTC
  • Shugaba Deby Ya Yi Wa Gwamnatinsa Garambawul

Shugaban Kasar Chadi Idris Deby ya yi garambawul a Majalisar ministocin sa, inda ya rage yawan su daga 37 zuwa 24 saboda abin da ya kira karancin kudin da gwamnati ke fuskanta.

Daga cikin sabin ministocin da aka nada akwai Mahamat Zene Cherif, Jakadan kasar a Majalisar Dinkin Duniya wanda yanzu ya karbi matsiyin  ministan harkokin wajen kasar , a yayin da Djimet Arabi, mai bai wa shugaban shawara  ya karbi matsayin  ministan shari’ar kasar.

Shugaba Idrisa Deby ya ce ya dauki wannan mataki ne domin rage yawan kudin da kasar ke kashewa saboda yanayin matsin tattalin arziki da kasar ke ciki.

Kasar Chadi na daya daga cikin kasashen da suka dogara da arzikin man fetur , amma saboda faduwar farashin man a kasuwannin duniya ya sanya kudaden da kasar ke samu ya ragu.