Kasashen Turkiyya Da Chadi Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Kasuwanci A Tsakaninsu
Dec 27, 2017 12:18 UTC
Kasashen Chadi da Turkiyya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar kasuwanci a tsakaninsu.
A ziyarar aikin da ya kai zuwa kasar Chadi: Shugaban kasar Turkiyya Rajab Tayyib Erdugan ya gana da takwararsa na kasar ta Chadi Idris Deby tare da cimma yarjejeniya a bangarori da dama da nufin bunkasa ci gaban kasashensu musamman a bangaren makamashi, masana'antu da sanya hannun jari a tsakaninsu.
Har ila yau shugabannin kasashen biyu sun yi tofin Allah tsine kan matakin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya dauka na shelanta birnin Qudus a matsayin fadar mulkin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila tare da bada umurnin maida ofishin jakadancin Amurka daga Tel-Aviv zuwa birnin Qudus.
Tags