Ci Gaba Da Komawar 'Yan Gudun Hijirar Siriya Zuwa Kasarsu
Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa: Al'ummar Siriya da suke zaune a kasar Lebanon a matsayin 'yan gudun hijira suna ci gaba da komawa kasarsu.
Kakakin Hukumar Kolin Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya Lisa Abou Khaled ta bayyana cewa: Dubban 'yan gudun hijirar Siriya da tashe-tashen hankula suka raba da muhallinsu kuma suka samu mafaka a cikin kasar Lebanon, suna ci gaba da komawa kasarsu, inda a halin yanzu aka kiyasta yawan mutanen da suka koma gida da cewa: Sun haura 500,000.
Lisa Abou Khaled ta kara da cewa: A watan Nuwamban da ya gabata an kiyasta cewa yawan 'yan gudun hijirar Siriya a cikin kasar Lebanon sun kai 997,905, don haka a ahalin yanzu kusan rabinsu sun koma kasarsu ta gado.