'Yan Kasar Congo Na Ci Gaba Da Kwarara Kasar Uganda
(last modified Wed, 27 Dec 2017 18:14:12 GMT )
Dec 27, 2017 18:14 UTC
  • 'Yan Kasar Congo Na Ci Gaba Da Kwarara Kasar Uganda

Babban kwamishinan dake kula da 'yan gudun hijra na MDD ya bayyana cewa daga ranar 18 ga watan Disemba zuwa yanzu sama da 'yan kasar D/Congo dubu hudu da 500 ne suka yi hijra zuwa kasar Uganda.

Cikin wata sanarwa da ya fitar a wannan laraba, Babban kwamishinan dake kula da 'yan gudun hijra na MDD Filippo Grandi ya bayyana cewa daga ranar 23 zuwa ranar 26 ga wannan wata na Disemba da muke ciki, sama da mutane dubu daya da 860 'yan kasar Congo suka rubuta sunayensu a sansanin 'yan gudun hijra na MDD dake kasar Uganda, wanda hakan ya sanya adadin 'yan gudun hijrar ya kai dubu 4 da 584 daga ranar 18 ga watan Disemba zuwa yanzu.

Sanarwa ta ce mafi yawa daga cikin 'yan gudun hijrar mata ne da kananen yara, da mafi yawansu ke shiga kasar ta Uganda ta hanyar tabkin Albert.

Sama da shekaru 20 kenan yankunan tsakiya, da gabashi gami da arewa maso gabashin kasar ta Congo ke fuskantar matsalar tsaro, kafin hakan a cikin watan Avrilun 2017 sama da fararen hula dubu 9 ne rikicin na Congo yayi sanadiyar tserewarsu zuwa kasar Uganda.