Pira Ministan Kasar Mali Ya Yi Murabus
Dec 30, 2017 10:20 UTC
Ofishin shugaban kasar ta Mali ya fitar da bayani da ya kunshi cewa; Pira minista Abdullah Idrisa Maiga ya yi murabus a jiya jumaa
Sanarwar ta kuma kara da cewa; Shugaban kasar ta Mali Ibrahim Bubakar Keita zai sanar da sunan sabon pira minista nan da wnai lokaci
Sai dai sanarwar ba ta kunshi dalilin da ya sa Pira ministan ya yi murabus din ba.
Kawo ya zuwa yanzu an kafa gwamnati hudu a karkashin shugaban kasa Ibrahim Bubakar Keita, wacce ta fara aiki tun 2013.
Kasar tana fuskantar matsalolin tsaro daga kungiyoyin da suke dauke da makamai a arewacin kasar.
Tags