An Bayyana Sabuwar Majalisar Zartar wa Ta Kasar Mali.
Sabon Firaministan kasar Mali ya fitar da sunayen manbobin Gwamnatinsa da ta kumshi ministoci 36
A wannan Lahadi, Sabon Firaministan kasar Soumeylou Boubèye Maiga ya fitar da sunayen sabin manbobin gwamnatin sa da ta kumshi ministoci 36 kwana guda kacal da Shugaban kasar Ibrahim Boubacar Kieta ya nada shi a matsayin sabon Firaministan kasar ta Mali bayan da tsohon Firaminista Abdoulaye Idriss Maiga da gwamnatinsa suka yi murabus.
A cikin manyan ma'aikatin sabuwar gwamnatin ta Mali, an nada Tiéna Coulibaly ministan tsaro, Timan Hubert a matsayin ministan harakokin wajen kasar, sai Bobo Sis da aka nada a matsayin ministan tattalin arziki da kudi, sannan kuma a nada hamidou youneseh maiga a ma'aikatar shara'ar kasar.
A ranar Juma'ar da ta gabata ce dai tsohon Firaministan kasar Abdoulaye Idriss Maiga ya yi murabus shi da gwamnatinsa ba tare da bayyana dalilinsa na yin hakan ba.
Sai dai wasu rahotanni daga kasar ta Mali na cewa bayan murabus din nasa zai jagoranci yakin neman zaben shugaba Ibrahim Boubacar Keita a zaben shugaban kasa a shekara mai zuwa.