Bukatar Kasar Uganda Ga Kasar Democcradiyyar Congo
(last modified Tue, 02 Jan 2018 11:48:58 GMT )
Jan 02, 2018 11:48 UTC
  • Bukatar Kasar Uganda Ga Kasar Democcradiyyar Congo

Sojojin kasar Uganda sun bukaci gwamnatin kasar Democradiyyar Congo ta basu damar shiga cikin kasar don bin sawon mayakan yan tawayen da suke sulalewa zuwa cikin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Xin huwa ta kasar China ya nakalto majiyar sojojin kasar Uganda tana cewa ta gabatar da bukata ga gwamnatin kasar Democradiyyar Congo ta basu damar shiga kasar don bin sawun mayakan kungiyar yan tawayen kasar ta "Hadaddiyar dakarun Democradia" wacce ake kira ADF.

Kafin haka ma, sojojin kasar Uganda, a ranar 22 ga watan Disamba shekarar da ta gabata sun kai hare-hare ta sama da ta kasa kan mabuyar yan tawayen a yankin KIVU ta arewa. 

Tun shekara ta 1994 ne yan tawayen na ADF suke amfani da arewacin kasar Congo wajen kai hare-hare a cikin kasar Uganda, inda suka salwantar da rayuka da dukiyoyi masu yawa.