Najeriya Za Ta Kara Kaimin Jigilar 'Yan Kasar Mazauna Kasar Libya
Jan 07, 2018 06:30 UTC
Ma'aikatar harkokin wajen Najeriya ta sanar a jiya asabar cewa za ta kara kaimin dawo da 'yan kasar daga Libya
Kamfanin dillancin labarun Faransa wanda ya nakalto bayanin ma'aikatar harkokin wajen ta Najeriya, ya ci gaba da cewa; Kasar za ta aike da jiragen sama biyu domin dauke yan kasar 800.
Tun bayan da tashar telbijin din CNN ta nuna yadda ake sayar da bakaken fata a cikin kasar Libya, kasar Najeriya ta fara mayar da yan kasarta gida daga Libyan, wanda kawo ya zuwa yanzu wadanda suka koma din sun kai 250
Tags